Hausa

Lauyoyi Sun Samu Ganawa Da Shaikh Zakzaky

— Saifullahi M Kabir

Mun samu labarin cewa jiya Litini da yammaci hukumar Nijeriya da suke tsare da Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun ga damar bari lauyoyinsa su gana da shi.

Kwamitin da ke fafutukar ganin an saki Shaikh Zakzaky sun bayyana a shafinsu na yanar gizo cewa, Lauyoyin wanda Femi Falana SAN ke jagorantarsu, sun gana da Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenat ne a ofishin DSS da ke Kaduna a yammacin jiya Litini 28/5/2018.

Wannan ganawar dai shine karo na uku tsakanin Shaikh Zakzaky da lauyoyinsa tun bayan kama shi da aka yi da tsare shi da hukumar kasar nan take yi a kusan tsawon shekaru biyu da rabi.

Tun dai ranar 15 ga watan Mayun nan ne hukumar kasar ta canzawa Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenat wajen tsarewa, inda a da ake tsare da su a Abuja, amma daga wannan ranar bayan fito da su daga kotun da aka kai su ana zarginsu da laifi a karon farko, ba a sake ganinsu ko jin labarin inda suke ba sai a jiyan.

Wasu na ganin cewa kai Shaikh Ibraheem Zakzaky, matarsa da wasu biyu daga almajiransa Kara da gwamnatin Kaduna ta yi tana cajinsu da aikata laifuka guda takwas, daga ciki har da zargin kashe wani soja mai suna Kofur DanKaduna, bayan abin da ya bayyana cewa sojoji sun kashe almajiransa fiye da 1000, da ‘ya’yansa da danginsa ba a Kuma kama Koda soja daya an zarge shi da laifi ba, na nufin wani sabon salon borin-kunya kuma sabon shafin zalunci da danniya.

Dadin abin shine, a kan kare a Duniyar, kuma a Lahira akwai hisabi. Ba inda ba Allah. Kuma shi ke kare bayinsa masu dogaro gare shi. Ya kasance yana daga kafa (Talala) ga azzalumai har su dauka cewa su ne masu iko. Kamunsa tabbatacce ne, kuma ba a jimawa.

IMN Ta Zargi Gwamnatin Buhari Da Kokarin Kawar Da Sheikh El-Zakzaky

Wani fitaccen malami, Sheikh Abdulhamid Bello ya zargi gwamnatin Buhari da yunkurin makarkashiya na kashe Sheikh El-zakzaky.

Sheikh Bello, wanda yake mamba ne na kungiyar ta El-Zakzaky ya bayyana hakan a yau Talata, 15 ga watan Mayu, 2018 inda yace “kwanaki 880 kenan da kama shugabanmu, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ba bisa kaida ba. Hakana kuma sati biyu kenan da kaimasa sammacen kotu, wanda shi kuma yaki sa hannu, ya kuma umarci hukuma da tayi abinda ya dace tukuna, ta bi umarnin kotu, ta sake shi”.

Sheikh Bello ya kara da cewa, abinda yake faruwa na baya-bayannan zai iya harzuka mabiyan kungiyar ‘yan-uwa musulmi (IMN), duba da irin abinda sojoji suka yiwa shugabannasu a watan Disambar 2015. Shehin yayi kira da kakkausar murya ga gwamnatin tarayya cewa itace alhakin duk abinda ya faru da shugabansu.

Rahoton HausaTv

Mu’assasar Shuhadah ta harkar Mudulunci a Najeriya ta bayyana ranar babban taron tunawa da Shahidai na bana

Mu’assasar Shahidai ta Harkar Musulunci a Najeriya shiyyar karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky ta bayyana ranar babban taron tunawa da shahidai na bana na shekarar 2018.

Taron aka shirya zai gudana ranar Alhamis nan mai zuwa 12 ga watan Aprilu, 2018.

Za a gabatar da taron ne a dandalin ‘yanci da aka fi sani da “Unity Fountain” dake birnin Abuja.

Kafin ranar, kamar yadda aka saba, za a gabatar da gagarumin Muzaharar kiran a gaggauta sakin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ranar Laraban nan mai zuwa bayan kammala zaman dirshan dake ci gaba da gudana a kullum a dandalin na “Unity Fountain”

A taron na bana, a kwai nazari na musamman sakamakon jimillan adadin Shahidan Harkar Musulunci da ya karu wanda hakan ya biyo bayan kazamin kisan kiyashin zariya na shekarar 2015 wanda Sojoji suka kashe daruruwan mabiya Harkar Musulunci cikin ‘yan sa’o’i karkashin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.